in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya fara gudanar da bincike kan batun samar da allurar rigakafin cututtuka maras inganci
2018-07-25 21:22:20 cri
A 'yan kwanakin nan, batun zargin samar da allurar rigakafin cutar cizon kare maras inganci da kamfanin kimiyya da fasahar halittu na Changsheng dake birnin Changchun ya yi, na jawo hankalin al'ummar kasar Sin sosai.

Game da wannan batu, a ranar 23 ga wata, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta tura wani rukuni zuwa kamfanin don gudanar da bincike. Kafin wannan, gwamnatin kasar Sin ta rigaya ta kame dukkan allurar rigakafin dake da nasaba da zargin, ta yadda ba za a ci gaba da yin amfani da su ba. Haka kuma, an dakatar da ayyukan wannan kamfani na samar da allurar rigakafi.

Yau Laraba ne kuma, hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta bayar da sanarwa, inda ta nuna cikakken goyon-baya da kuma yabawa matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka ba tare da bata lokaci ba, kuma ba tare da rufa-rufa ba. Inda ta ce, wannan batu ya bakantawa jama'a rai, amma an tona asirin ne sakamakon binciken ba zata da aka yi, al'amarin da ya shaida cewa, tsarin sa ido kan ayyukan kamfanonin, gami da binciken da aka yi, na iya kare lafiyar jama'a a kasar Sin.

A baya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin wanda a yanzu haka ke ziyara kasashen Afirka, ya bada umurni yana mai cewa, ya kamata a binciki musabbabin lamarin daga tushe, da yanke hukunci mai tsanani kan mutanen da suka aikata laifi. Xi ya jaddada cewa, ya kamata a mayar da lafiyar jama'a a gaban komai, da kyautata tsarin sa ido kan ayyukan samar da allurar rigakafi, gami da tabbatar da tsaro.

Shi kuma a nasa bangaren, firaministan kasar Sin Li Keqianig ya bukaci a gudanar da bincike daga tushe, kan dukkanin ayyukan da suka shafi samarwa gami da sayar da allurar rigakafi.

Rukunin majalisar gudanarwa ta kasar Sin zai gudanar da ayyukansu daga wasu muhimman fannoni bakwai. Na farko shi ne bincikar ayyukan kamfanin Changsheng wadanda suka sabawa doka. Na biyu, a yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka aikata laifi. Na uku, a binciki ayyukan da ma'aikatan gwamnati suka yi, da dora alhaki kan wadanda suka nuna sakaci wajen aiki. Na hudu, a bullo da matakan tallafawa mutanen da suke da bukata. Na biyar, a daidaita matsalolin kamfanin da abun ya shafa. Na shida, a maida martani kan abubuwa da suka jawo hankalin jama'a. Na bakwai wato na karshe shi ne, a yi gyare-gyare, gami da kyautata tsarin sa ido kan ayyukan samar da allurar rigakafi.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China