in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya nuna damuwa game da hasarar rayuka a ballewar dam a Laos
2018-07-25 10:29:38 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya bayyana alhini game da hasarar rayuka da aka samu da kuma mummunar barnar da madatsar ruwa ta haifar a lokacin gina aikin samar da lantarki ta ruwa a kasar Laos ta nahiyar Asiya.

Kakakin MDDr Stephane Dujarric, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, mista Guterres ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda iftila'in ya rutsa da su, da kuma jajantawa gwamnati da al'ummar kasar Laos, kana ya jaddada aniyar MDDr ta bayar da tallafin aikin ceto, da kuma samar da kayan tallafin jin kai idan bukatar hakan ta kama.

Mutane da dama ne dai suka hallaka, kana wasu daruruwa kuma suka bace bayan da madatsar ruwan ta balle da yammacin ranar Litinin a lardin Attapeu dake kudancin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China