in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron dandalin tattaunawa tsakanin al'ummomin Sin da Afirka karo na 5
2018-07-24 16:56:24 cri

A yau ne, aka rufe taron dandalin tattaunawa tsakanin al'ummomin Sin da Afirka karo na 5 a birnin Chengdu, wanda kungiyar kula da harkokin mu'amala tsakanin al'ummomin kasar Sin da na ketare da gwamnatin lardin Sichuan suka shirya cikin hadin gwiwa. A yayin bikin rufe taron an kuma gabatar da "shirin abota tsakanin al'ummomin Sin da Afrika na shekarar 2018 zuwa 2020".

Shirin da aka gabatar bayan tattaunawa mai zurfi tsakanin kungiyoyin kula da harkokin yin mu'amala tsakanin al'ummomin Sin da Afirka, ya kunshi ayyukan hadin kai tsakanin al'umomin Sin da Afrika guda 30, da ya shafi fannoni biyar, ciki har da hada kai a fannin zaman rayuwar jama'a, da ba da tallafi, yin mu'ammalar masana da kwararru, kokarin samun bunkasuwa, da mu'ammalar al'adu da bullo da tsarin tuntubar juna da dai sauransu, wanda ya shata taswirar hadin kai tsakanin al'ummomoin bangarorin biyu cikin shekaru 3 masu zuwa.

Rahotanni na cewa, wannan dandali daya ne daga cikin ayyukan taron ministocin dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika. Taron na wannan karo ya samu halartar wakilai fiye da 200 daga kungiyoyin al'ummomin kasar Sin da na kasashen Afirka 123 na Sin da kasashen Afirka 30. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China