in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kasa da kasa na yaki da cutar AIDS na 2018 a Amsterdam
2018-07-24 10:36:47 cri

Da yammacin ranar Litinin aka bude taron kasa da kasa karo na 22 na yaki da cuta mai karya garkuwar jiki wato AIDS na shekarar 2018 a birnin Amsterdam, babban abin da taron zai fi mayar da hankali ya hada da sabbin hanyoyin zuba jarin yaki da cutar, matakan kimiyya, da dabarun siyasa da ake bukatar amfani da su wajen kawar da kwayar cutar ta HIV.

Shugabar hukumar yaki da cutar ta kasa da kasa (IAS), kana shugabar taron yaki da cutar na bana Linda-Gail Bekker, ta ce, babban shamakin da ake samu a halin yanzu a kokarin kawar da cutar shi ne, irin tunanin da ake amfani da shi da matakan siyasa da ake bi wajen yaki da cutar. Ta hanyar hadin gwiwa, za'a bukaci masanan dake tsara dabaru da kungiyoyin dake ba da agajin yaki da cutar da su bayar da shedu, kana za'a kawar da cutar ne ta hanyar tsara manufofin da suka dace, da samar da isassun kudade, da yin aiki tukuru, ta yadda ba za'a bar wani bangare a gefe ba.

Taron na kasa da kasa na yaki da cutar ta AIDS shi ne taro mafi girma game da yaki da cutar ta AIDS da aka gudanar a duniya. Taron na wuni biyar, zai gabatar da sabbin hanyoyin kimiyya da fasaha wajen warkar da masu dauke da cutar, da bayar da magani da yin rigakafi da sabbin dabarun da za'a yi amfani da su wajen cimma nasarar yaki da cutar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China