in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da tabbatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya" don kawo alfanu ga duniya
2018-07-24 10:12:19 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya yi bayyani kan wasu takardun hadin kai da Sin ta kulla da kasashen dake cikin shawarar "Ziri daya da hanya daya", lokacin da shugaba Xi Jinping ya kai ziyara hadaddiyar daular Larabawa UAE da Senegal da sauran kasashe, inda ya ce, Sin za ta ci gaba da hada kai da sauran kasashe da kuma kungiyoyin kasa da kasa bisa ka'idar yin shawarari da kawo moriyar juna don tabbatar da cewa shawarar ta taimaka ga zaman lafiyar duniya da shiyya-shiyya da bunkasuwar duniya mai wadata.

Geng Shuang ya bayyana hadaddiyar daular Larabawa a matsayin muhimmiyar kasa wajen raya yankin da shawarar ta shafa, ya kuma bayyana fatan ganin ta shiga aikin gina shawarar ta Ziri daya da hanya daya.

Yayin ziyarar ta shugaba Xi, bangarorin biyu sun nanata hadin gwiwa tsakaninsu bisa wannan shawara, da kara tuntubar juna da zurfafa hadin kai ta fuskar samar da kayayyaki, da kuma kokarin samun ci gaba mai armashi a dukkanin fannoni tsakanninsu.

Hakazalika, Geng ya ce, yayin ziryar shugaba Xi a Senegal, shugaba Macky Sall ya nuna cewa, Senegal na goyon bayan wannan shawara sosai, kuma tana sa ran shiga a dama da ita wajen kara tuntubar juna a dukkanin fannoni. Ban da wannan kuma, shugabannin biyu sun kalli sa hannu kan takardun hadin kai game da wannan shawara. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China