in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta dora alhakin karancin samun bayanai wajen haifar da gibin ciniki a tsakanin kasashen Afrika
2018-07-24 10:07:44 cri

A jiya Litinin kungiyar tarayyar Afrika AU ta dora alhakin karancin musayar bayanai game da damammakin kasuwanci a matsayin babban abin da ke haddasa koma baya na rashin yin mu'amalar ciniki a tsakanin 'yan kasuwar kasashen nahiyar Afrika.

Albert Muchanga, kwamishinan AU mai kula da sha'anin ciniki da masana'antu, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, mu'amalar cinikayyar dake gudana a tsakanin kasashen Afrika da junansu ba ta kai kaso 18 bisa 100 ba, kuma wannan shi ne cinikayya mafi kankanta dake gudana a tsakanin wata shiyya guda a duniya.

Muchanga ya ce, za su ci gaba da kokarin sanya ido da samar da farashin kayayyakin da aka fi bukata da ayyukan hidima a duk fadin Afrika, domin hakan ya ba su damar bunkasa mu'amalar cinikayya a tsakanin kasashen na Afrika.

Ya ce, idan aka samu ingantattun bayanai, nahiyar za ta iya bunkasa cinikayya a tsakanin kasashen Afrikan wanda zai iya kaiwa kashi 50 bisa 100 a cikin kankanin lokaci, kuma hakan zai rage yawan kudaden harajin shigo da kayayyaki da ake kuka da shi, inda kasashen za su samu damar yin cinikayya a tsakaninsu cikin sauki.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China