Ya ce dole ne kananan hukumomin da lamarin ya shafa su mai da hankali a kai, su yi bincike ba tare da bata lokaci ba. Kana su yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka aikata laifukan. Xi ya jaddada cewa, kamata ya yi a mai da kiwon lafiyar jama'a a gaban kome a kuma ko yaushe. Kaza lika a kyautata tsarin gudanar da harkokin allurar rigakafin cututtuka, don ba da tabbaci ga babbar moriyar jama'a, da zaman karkon al'umma. (Bilkisu Xin)