in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Tunisiya ya yabawa taimakon Sin na gina asibiti a gabashin kasar
2018-07-23 10:07:33 cri

Daraktan kiwon lafiya na shiyya a yankin Sfax na kasar Tunisiya Ali Ayadi ya ce, asibitin da ake ginawa bisa tallafin kasar Sin a yankin Sfax dake gabashin kasar ya nuna irin kyakkyawar nasarar da aka samu ta hadin gwiwar kasar Tunisiya da kasar Sin a fannin kiwon lafiya.

Jami'in sashen ciniki da tattalin arziki na ofishin jakadancin kasar Sin a Tunisiya Zhang Fengling ya ce, suna fatan ganin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Tunisiya a fannin kiwon lafiya ya kai matsayin koli.

An fara aikin ginin ne a watan Disambar shekarar 2016, kuma ana sa ran kammala aikin a karshen shekarar 2019, asibitin zai kasance cibiyar musamman ta kula da masu fama da ciwon zuciya.

Asibitin yana da girman murabba'in mita 26,000, kuma yana da gadaje kimanin 250, akwai sashen tiyata, da dakunan fida 5, da sashen ba da kulawar gaggawa, da cibiyar daukar hoton kirji da cibiyar ba da magunguna da sauransu.

A watanni hudun farkon wannan shekarar, tawagar jami'an kiwon lafiya ta kasar Sin dake Tunisiya ta bayar da aikin jiyya kimanin 18,000, kana sun gudanar da aikin tiyata guda 1,559 a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China