in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 11 sun hallaka a harin kunar bakin wake a Kabul
2018-07-23 10:00:48 cri

Kakakin hukumar 'yan sanda a Afghanistan Hashmat Stanikzai ya ce, mutane 11 ne suka mutu, kana wasu 14 kuma suka jikkata a wani harin kunar bakin wake da aka kaddamar a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan a jiya Lahadi.

A cewar jami'in, harin kunar bakin waken ya auku ne da misalin karfe 5 na yammaci, agogin yankin a kan titin zuwa filin jirgin saman kasa da kasa na Kabul, a daidai lokacin da tawagar mataimakin shugaban kasar Afghanistan na I Janar Abdul Rashid Dostum yake wucewa ta yankin.

Jami'in ya ce, dukkan wadanda harin ya rutsa da su fararen hula ne sai wani jami'in dan sanda guda daya.

A cewar hukumar asibitin, mutane 48 ne suka samu raunuka, kuma tuni aka garzaya da su asibitocin don ba su kulawa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China