in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CMG na kasar Sin da gidan talabajin na kasar Senegal sun kulla yarjejeniyar "watsa wasan kwaikwayon Sin"
2018-07-21 18:04:57 cri
A ranar 19 ga wata, an yi bikin fara shirin "watsa fina-finai da wasan kwaikwayo na kasar Sin a kasashen Afirka" a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal. Shugaban babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice na yankin Turai ta yamma Gao Shijun, ya halarci bikin inda aka kulla yarjejeniyar "kafa shirin nune-nunen fina-finai da wasannin kwaikwayon Sin" tare da shugaban babban gidan talabijin na kasar Senegal Racine Talla.

Bisa yarjejeniyar, babban gidan talabijin na kasar Senegal zai kafa wani shirin nune-nunen "fina-finai da wasan kwaikwayo na kasar Sin", inda zai watsa fina-finai da shiye-shiryen wasan kwaikwayo na kasar Sin, wadanda aka fassara su zuwa harshen Faransanci. Kuma a karon farko, za a watsa wasan kwaikwayo na talabijin guda daya, shirye-shiryen labarum tarihi guda biyar, da kuma fina-finan cartoon guda biyar.

Ban da haka kuma, kamfanin Star Times zai gabatar da shirye-shiryen wasan kwaikwayon talabijin da fina-finai da dama a kasar Senegal da wasu kasashen Afirka masu amfani da harshen Faransanci, sakamakon samar da talabijin dake aiki da tauraron dan Adam a garuruwa sama da dubu 10 na kasashen Afirka, wanda aka tsara bisa manyan shirye-shirye guda goma na hadin gwiwar Sin da Afirka.

Wakilin ofishin watsa labarai na gwamnatin kasar Sin Zhang Yanbin, da ministan harkokin labarai na kasar Senegal Abdoulaye Bibi Balde, da jakadan kasar Sin dake kasar Senegal Zhangxun da dai sauran wakilai na kafofin yada labarai sama da dari 1 sun halarci wannan bikin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China