in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron karawa juna sani mai taken "Ra'ayin Xi Jinping na kawar da talauci da hadin gwiwar Sin da Afirka don neman ci gaba" a Senegal
2018-07-21 15:14:55 cri
A ranar Alhamis 19 ga watan nan ne aka kammala taron karawa juna sani mai taken "Ra'ayin Xi Jinping na kawar da talauci, da hadin gwiwar Sin da Afirka don neman ci gaba" a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal.

Taron da aka gudanar bisa hadin gwiwar ofishin watsa labarai na gwamnatin kasar Sin, da cibiyar nazarin ilmin zaman takewar al'umma ta Sin, da ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Senegal, da ma'aikatar harkokin ba da ilmi, yin nazari, neman sabuntawa ta kasar Senegal, da kuma jami'ar Dakar, ya samu halartar firaministan kasar Senegal Mahammed Boun Abdallah Dionne, da ministan harkokin ba da ilmi da yin nazari na kasar Mary Teuw Niane, da wakilin ofishin labarai na gwamnatin kasar Sin Zhang Yanbin, da kuma jakadan kasar Sin dake kasar Senegal Zhang Xun, da dai sauran wakilan Sin da na kasashen Afirka kimanin dari 2.

A yayin dake ba da jawabi, firaministan kasar Senegal Mahammed Boun Abdallah Dionne, ya yaba wa kasar Sin kan muhimmiyar rawa da ta taka wajen kawar da talauci, yana ganin cewa, hakan ya kasance abin koyi ga kasa da kasa. Sa'an nan, ya kuma nuna yabo ga manufofin da aka tsara wajen kawar da talauci bisa jagorancin shugaba Xi Jinping, wadanda suke da muhimmiyar ma'ana wajen karfafa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a fannin kawar da talauci.

Bugu da kari, ya ce, gwamnati da dukkanin al'ummar kasar Senegal, suna sa ran zuwan ziyarar da shugaba Xi zai kai kasar, domin tabbas ne, ziyarar tasa ta wannan karo, za ta daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Haka kuma, a yayin taron, wakilai da masana na kasashen Sin da Afirka, sun yi tattaunawa mai zurfi kan ra'ayoyin Xi Jinping na kawar da talauci, da kuma hadin gwiwar Sin da Afirka kan wannan aiki, inda suka cimma matsayi daya kan batutuwa da dama, lamarin da ya kasance babban goyon baya ga ci gaban hadin gwiwar Sin da Afirka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China