in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin kasar Amurka dake kasar Sin sun samu babbar moriya
2018-07-20 11:08:37 cri
Kwamitin kula da aya mai lamba 301 na kasar Amurka, zai gudanar da taron sauraron ra'ayoyin jama'a tun daga ranar 20 zuwa 23 ga watan Agusta, inda za a tattauna game da jerin sunayen hajojin, da za a kara karbar harajin kwastam na kashi 10 cikin dari, kan kayayyakin Sin da ake shigarwa kasar Amurka, wadanda yawansu ya kai dala biliyan 200 da aka fitar a ranar 10 ga watan Yuli.

Gwamnatin Trump ta bayyana cewa, dalilin da ya sa ta yi hakan shi ne, dakile rashin daidaito, da ciniki maras adalci da kasar Sin take aiwatarwa, ciki har da rangwame da gwamnatin kasar ke bayarwa wanda ya haifar da hasarori ga kasar Amurka.

Daga ra'ayin gwamnatin Trump kadai, ana iya gano cewa, kasar Amurka ta samu hasara ne bisa yanayin cinikayyar ta da kasar Sin, kana Sin tana nuna rashin adalci ga kamfanonin Amurka. Amma a hakika batun ba haka yake ba.

Da farko dai, a sakamakon bunkasuwar tattalin arzikin Sin cikin sauri da fadadar kasuwa, kamfanonin kasar Amurka da dama sun cimma nasarori a kasuwar kasar Sin.

Na biyu, kananan gwamnatocin kasar Sin su kan gabatar da manufofin nuna gatanci a fannonin haraji, da hada-hadar kudi, da yankunan kasa, da sauransu, don sa kaimi ga kamfanonin kasashen waje, wajen zuba jari a yankin yammaci da tsakiyar kasar Sin maras samun ci gaba, ko raya wasu sana'o'i.

Ga kamfanonin kasar Amurka da suka zuba jari a kasar Sin, manufofin da aka gabatar, da kudin da aka nuna goyon bayansu wajen sa kaimi gare su sun haifar da bunkasuwa da babbar moriya.

An yi hasashen cewa, kasar Sin za ta zarce kasar Amurka, wajen zama kasuwa mafi girma a duniya a shekarar 2018. Wannan ya shaida cewa, kamfanonin kasa da kasa, za su yi kokarin shiga kasuwar kasar Sin, ciki har da kamfanonin kasar Amurka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China