Yayin taron manema labarai, Gao ya bayyana cewa, a zaman bitar da aka yi, akasarin membobi suna yaba matuka ga bunkasuwar manufofin cinikayya da irin ci gaban da kasar Sin ta samu, haka kuma sun yabawa kasar saboda gudummawa da muhimmiyar rawar da ta taka wajen tabbatar da tsarin cinikayya dake kunshe da bangarori da dama. Mambobin na ganin cewa, raya tattalin arziki gami da aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ke yi, na samar da babban zarafi ga sauran kasashe don samun bunkasuwa. (Murtala Zhang)