Rahotannin da aka ruwaito sun ce, kwanan baya, mai taimakawa sakataren harkokin wajen Amurka kan harkokin tsaro da hana yaduwar makamai ya bayyana cewa, da gangan kasar Sin ta yi yunkurin samo fasahohin zamani na Amurka ta hanyar yin hadin-gwiwa ta fannin yin amfani da makamashin nukiliya a kan wasu ayyukan da ba na soja ba, gami da yin amfani da su a fannin ayyukan soja, domin taimaka mata wajen yin takara e da sauran kasashe. Game da wannan kalamai, Madam Hua ta nuna cewa, kasar Sin na adawa da yaduwar makaman kare-dangi da ma na'urorin jigilarsu, kuma ta cika alkawarin da ta dauka na haramta yaduwar makamai a fadin duniya. A 'yan shekarun nan, kasar Sin ta bullo da wani cikakken tsari na hana yaduwar makamai, da sa ido kan kayayyakin da take fitarwa zuwa kasashen waje, ko a harkokin cikin gida, ko a harkokin fitar da kayayyaki, gwamnatin Sin na daukar kwararan matakai, da kare tsarin hana yaduwar makamai na duniya, da kuma bayar da muhimmiyar gudummawa wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya. (Murtala Zhang)