in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Japan da EU sun yi hadin gwiwar cinikayya tsakaninsu cikin 'yanci, ko suna son yi wa Amurka bore ne?
2018-07-18 21:00:02 cri
A jiya Talata 17 ga watan Yulin nan ne kafofin watsa labarun kasar Japan, suka mai da hankulansu kan kalmomin "nuna adawa da Amurka", da "yin cinikayya cikin 'yanci" da "habaka abokan cinikayya" da dai makamatansu a labaran da suka watsa.

A wannan rana, kungiyar kasashen Turai, wato EU da kasar Japan sun rattaba hannu kan "yarjejeniyar tabbatar da huldar abokantaka ta fuskar tattalin arziki ko EPA a takaice". Wannan yarjejeniya ce ta yin cinikayya cikin 'yanci mafi girma da aka kulla, an kuma yi hasashen cewa, yarjejeniyar za ta fara aiki a cikin shekarar nan da muke ciki.

Idan yarjejeniyar ta fara aiki, to, za a samu yankin cinikayya cikin 'yanci mafi girma a duk fadin duniya, mai kunshe da mutane miliyan 600, kuma yawan GDPn sa zai kai kaso 30% idan an kwatanta da na duk sauran sassan duniya.

To ko mene ne dalilin da ya sanya kasar Japan da kawancen kasashen Turai suka kulla wannan yarjejeniyar yin cinikayya cikin 'yanci yanzu? Kuma don me suka sha daukar matakai daban daban wajen ingiza manufar yin cinikayya tsakanin bangarori daban daban a 'yan watannin baya bayan nan?. Ko shakka babu, wannan yarjejeniya tana cikin shirin da kasar Japan ta tsara game da ayyukan diflomasiyya da za ta yi a bana. Sannan, tana fatan yin hadin gwiwa da kasashen Turai, domin nuna adawa da matakan kakaba takunkumi da kasar Amurka take yi mata, ta yadda za ta iya habaka, da kuma karfafa tushen tattalin arzikinta da ta bunkasa a ketare.

Da farko dai, bunkasa cinikayya ba tare da shinge ba tsakanin bangarori daban daban, babbar manufa ce da kasar Japan take bi. Bayan da Donald Trump ya hau kan mukamin shugabantar kasar Amurka, yana kokarin aiwatar da manufarsa ta "sanya kasar Amurka a gaban kome," hakan ya sa ya nuna adawa da manufar yin cinikayya cikin 'yanci, ya daukar matakai iri iri bisa radin kan sa, har ma ya yi watsi da wasu yarjejeniyoyin da aka tsara a tsakanin kasar Amurka da wasu daban, ko tsakanin kasashe daban daban.

Bisa wannan yarjejeniyar da ta kulla da kawancen kasashen Turai, kasar Japan tana son yin amfani da karfin matsakaita, da kananan kasashen da yarjejeniyar za ta shafa, wajen karfafa karfinta ta fuskokin tattalin arziki da siyasa. Sabo da haka, aka bayyana cewa, a fili take cewa, kasar Japan tana martaba kasar Amurka, amma a hakika, wannan wani muhimmin mataki ne da kasar Japan ta dauka domin nisanta ta da kasar Amurka.

Daga bisani kuma, kasar Japan tana kokarin habaka kasuwannin tattalin arzikinta a kasashen ketare, da kuma karfafa huldar tattalin arziki dake tsakaninta da kasashen ketare, domin fuskantar kalubalolin takunkumin da kasar Amurka ta kakkaba mata, da na shawarwarin cinikin dake tsakaninsu.

A yayin da aka gudanar da babban zaben shugaban kasa a Amurka, Donald Trump ya taba bayyana rashin gamsuwarsa kan kasar Japan.

Ya ce kasar Japan ta samun moriya, amma kasar Amurka na kashe kudi a fannin ciniki. Kana, ya nuna cewa, bayan ya kama ragamar mulkin kasarsa, ba zai nuna hakuri ko kadan ba, kan babbar rarar kudin da kasar Japan ta samu daga kasar Amurka.

Sa'an nan, bayan Donald Trump ya fara aikin shugabancin kasa, ya fara matsa wa kasar Japan lamba da ta yi shawarwari da kasarsa, kan harkokin ciniki, domin rage rarar kudin da kasar Japan ta samu.

A nata bangare kuma, gwamnatin dake karkashin jagorancin Shinzo Abe ta ci gaba da inganta yarjejeniyar hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin kasar Japan da kasashen Turai, domin mai da martani kan gwamnatin kasar Amurka, da kuma habaka tattalin arzikin kasar Japan a kasuwannin duniya. Haka kuma, shirin gwamnatin kasar Japan shi ne, ci gaba da habaka tattalin arzikinta a kasuwannin duniya, ta yadda za ta iya karfafa karfin siyasarta tsakanin kasa da kasa.

Japan ta rattaba hannu kan yarjejeniyar EPA tare da kungiyar EU ne bisa la'akari da manyan tsare-tsarenta. Japan na dogaro kusan kacokan kan Amurka, a fannonin da suka shafi tsaron siyasa da aikin soja, in ba don kakabawa Japan da tarayyar Turai takunkumin ciniki da gwamnatin Trump ta yi ba, Japan da tarayyar Turai ba za su yi "bore" ba. A kwanakin baya ne, Japan ta daddale wasu yarjejeniyoyin hadin-gwiwar ciniki da dama, al'amarin da ya shaida babbar niyyarta ta yin watsi da dogaronta kan Amurka, da farko a fannin tattalin arziki, daga baya kuma sai fannonin siyasa da diflomasiyya. Wannan dabara ce da Japan ke amfani da ita wajen yaki da Amurka.

Bayan da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar EPA, firaministan kasar Japn Shinzo Abe, da shugaban majalisar tarayyar Turai Donald Franciszek Tusk sun fitar da sanarwar dake cewa, yarjejeniyar ta shaidawa duniya cewa, Japan da tarayyar Turai wato EU, za su ci gaba da daga tutar gudanar da cinikayya cikin 'yanci. Ana ganin cewa, sun yi wannan furuci ne domin maida martani kan matakan da gwamnatin Trump ta dauka. Babu tantama, kara nuna fin karfin da Amurka ke yi a fannin cinikayya zai kawo baraka a tsakanin kasashen dake cikin kawancenta a yammacin duniya. (Sanusi Chen, Maryam Yang, Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China