in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gudanar da yakin cinikayya ya sa Amurka ta nunawa duk duniya kiyayya, in ji ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin
2018-07-18 19:59:33 cri
A yau Laraba ne mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying ta ce, ba domin kasar Sin kawai Amurka take yin yakin cinikayya ba, domin Amurkar ta zama mai nuna kiyayya a dukkanin duniya, kana, za ta sa tattalin arzikin duniyar ya tsunduma cikin hadari.

Rahotanni sun nuna cewa, yakin cinikayya da Amurka ta kaddamar na janyo damuwa ga kasashe daban-daban. Game da wannan batu, Hua Chunying ta ce, Amurka ta kaddamar da yakin ne saboda kare muradun kanta, ba tare da la'akari da moriyar sauran kasashe ba. Kuma idan ta ci gaba da yin haka, za ta haifar da babbar illa ga tattalin arzikin duk duniya.

Madam Hua ta kara da cewa, yakin cinikayyar dake dada kamari zai raunata imanin kasashe daban-daban kan tattalin arzikin duniya, zai kuma yi illa ga moriyar al'ummar duniya.

Bisa hasashen da aka yi, an ce, sakamakon kara sanya harajin kwastam da wasu kasashe suka yi, saurin karuwar tattalin arzikin duniya zai ragu da kashi 1.4 bisa dari. Har ma cibiyoyin tattalin arzikin Amurka sun yi hasashen cewa, yakin cinikayya zai sa 'yan kasar dubu 600 rasa guraban ayyukan yi.

Har wa yau, rahotannin sun ce, mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence ya ce, kasarsa za ta dauki kwararan matakai don hana kasar Sin "sace" fasahohi. Game da haka, Madam Hua ta nuna cewa, zargin da Amurka ta yiwa kasar Sin na cewa wai tana "satar" ikon mallakar ilimi, tamkar rikida tarihi, da yanayin da ake ciki yanzu ne da Amurka take yi.

Ya ce nasarorin da kasar Sin ta samu ba don sace wani abu ko kuma kwace wani abu daga sauran kasashe ba ne, hakan ya biyo bayan himma da kwazon da daukacin jama'ar kasar Sin suka nuna ne. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China