Da yake nuna yabo ga dadaddiyar huldar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu, Song ya ce, jam'iyyar CPC a shirye take ta kyautata mu'amala tsakaninta da jam'iyya mai mulkin kasar Tanzaniya wato jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi (CCM), da kuma yin koyi da juna a tsakanin jam'iyyun.
Kasar Sin za ta cigaba da mutunta tsarin mu'amala bisa gaskiya, samun sakamako na hakika, kaunar juna, da kuma nuna fatan alkhairi ga manufofin kasar ta Afrika, wanda shi ne babban abin da shugaba Xi Jinping ya sanya a gaba, da kuma daga matsayin huldar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki, in ji Song.
A nasa bangaren, Magufuli ya ce jamiyyar CCM za ta cigaba da tabbatar da kiyaye al'adar mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma kara karfafa matsayin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Ahmad)