in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana iya dakile kalubalen rashin tabbacin tattalin arzikin duniya
2018-07-18 11:08:14 cri

Jiya Talata a nan birnin Beijing, kakakin watsa labarai na hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasarsa tana cike da imani kan ci gaban tattalin arzikinta, tabbas ne za ta cimma burin raya tattalin arzikin kasar data tsara a farkon wannan shekara, haka kuma tana iya dakile kalubale da rashin tabbacin tattalin arzikin duniya zai kawo mata.  

Bisa alkaluman da aka fitar ba da dadewa ba, an ce, adadin GDP na farkon rabin shekarar bana na kasar Sin ya karu da kaso 6.8 idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin bara, wato adadin karuwar ya rike kai kaso 6.7 zuwa 6.9 bisa dari a cikin rubu'i 12 da suka gabata, game da wannan, kakakin watsa labarai na hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin Yan Pengcheng ya bayyana cewa, alkaluman sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana samun ci gaba cikin sauri kuma cikin kwanciyar hankali, hakan shi ma ya samar da sharadi mai kyau ga kasar ta Sin wajen dakile kalubale da rikici a fannoni daban daban. Kana an yi hasashen cewa, tun daga watan Yuli har zuwa karshen bana, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun bunkasuwa sannu a hankali, a cewarsa: "A halin da ake ciki yanzu tsarin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ya sauya, a baya an dogara ne kan zuba jari da kuma fitar da kayayyaki zuwa ketare, amma yanzu aikin sayayya da aikin hidima da bukatun gida suna kara taka rawa yayin da ake kokarin raya tattalin aziki a kasar, har adadin kudin da aka samu daga wajen sayayya da hidima ya kai kaso 60 bisa dari, adadin kudin da aka samu daga wajen cinikayyar waje yana raguwa a kai a kai, adadin mutanen kasar da suka shiga kasuwa ya karu da kaso 80 bisa dari a cikin shekaru biyar da suka gabata kawo yanzu adadin ya riga ya kai miliyan 100, kana sabbin sana'o'in da ake gudanarwa a kasar suna samun ci gaba cikin sauri, haka kuma sabon karfin da aka sanyawa karuwa tattalin arzikin yana kara karuwa har ya kai kashi 1 bisa 3."

Ban da haka kuma, gwamnatin kasar Sin tana kara bude kofa ga kasashen waje, muhallin cinikayya ma ya samu kyautatuwa a bayyane, ta haka ya kara jawo hankalin kamfanonin jarin waje a fadin duniya, misali a farkon rabin shekarar bana, adadin sabbin kamfanonin jarin wajen da aka kafa a kasar Sin ya karu da kaso 96.6 bisa dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin bara, duk wadannan zasu bada tabbaci mai karfi ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.

Yan Pengcheng ya jaddada cewa, yanzu gibin kasafin kudin kasar Sin da bashin gwamnatin kasar sun yi rugu matuka, kudin da aka adana a cikin bankin kasuwancin kasar ya yi yawa, bashin kamfanonin kasar shi ma ya ragu, ana iya cewa kasar Sin tana iya dakile kalubale na rikici da rashin tabbacin tattalin arzikin duniya zai iya kawo mata ta hanyar aiwatar da manufa bisa manyan tsare tsare, yana mai cewa, "Nan gaba zamu kara maida hankali kan harkar zuba jari da kyautata tsarin sayayya domin biyan bukatun gida, kana zamu ci gaba da sanya kokari kan aikin yin gyaran fuska a muhimman fannoni, domin tabbatar da kirkire-kirkire, tare kuma da gudanar da kasuwa yadda ya kamata, banda haka kuma, zamu kara kyautata muhallin cinikayya da rage harajin da ake karba daga wajen kamfanoni, ta yadda kamfanonin zasu iya samun ci gaba lami lafiya, kazalika kasar Sin zata kara bude kofa ga ketare, domin kara samun jarin waje, a sa'i daya kuma, zamu nuna goyon baya ga kamfanonin da suke gamuwa da matsala a sanadin ringimun tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka,."

Jami'in ya bayyana cewa, kasar Sin tana da tsarinta na musamman, tana iya tattara daukacin albarkatun kasa domin gudanar da wani babban aiki, misali a cikin shekaru 40 da suka gabata wato tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima da bude kofa ga ketare a kasar ta Sin, kasar Sin ta taba yin nasara kan aikin dakile rikicin kudin kasashen Asiya a shekarar 1997 da rikicin kudin kasashen duniya a shekarar 2008 da sauransu, don haka kasar ta Sin ta tattara fasahohi da dama a fannin, a cewarsa: "A takaice dai, muna cike da imani kan karfinmu wajen dakile kalubalen da rashin tabbacin cigaban tattalin arzikin duniya zai kawo mata, ko shakka babu kasar Sin zata cimma burin raya tattalin arzikin kasar data tsara a farkon shekarar da muke ciki."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China