in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kolin tattaunawa tsakanin jamiyyar CPC da jamiyyun kasashen Afrika a Tanzania
2018-07-18 10:37:16 cri

Jiya Talata aka bude taron koli na wuni biyu na tattaunawa tsakanin jami'an jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) da wasu jam'iyyun siyasa da kungiyoyi kimanin 40 daga kasashen Afrika akalla 40 a Dar es Salaam birnin kasuwancin kasar Tanzaniya.

Jam'iyyun siyasar daga kasashen Sin da Afrika, su ne ke da ikon daga matsayin dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika, inji Song Tao, shugaban sashen hulda da kasa da kasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, wanda ya bayyana hakan a lokacin bude taron kolin tattaunawar jam'iyyar ta CPC da jam'iyyun siyasar kasashen na Afrika.

Song ya ce, jam'iyyar CPC a shirye take ta yi aiki tare da jam'iyyun siyasar kasashen Afrika wajen daga matsayin gina al'umma mai kyakkyawar makoma bisa ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika.

Ya bukaci a mayar da hankali wajen samar da cigaban da zai shafi rayuwar al'umma, ya kara da cewa, jam'iyyar CPC tana mayar da hankali ne game da batutuwan da suka shafi cigaban al'umma, da kuma zurfafa yin gyare gyare da bude kofa ga dukkan bangarori.

Shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli, ya bayyana cewa, zabar kasashen Afrika da kuma Tanzania a matsayin wajen gudanar da taron kolin tattaunawar na jam'iyyar CPC da jam'iyyun siyasar Afrika ya nuna yadda CPC ke daukar kasashen Afrika da muhimmanci da kuma yadda kasar ke martaba huldar abota dake tsakanin Sin da Tanzaniya. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China