Wang Yi ya bayyana lafiya a matsayin jigo ga mu'amalar al'ummar duniya, kuma tushen ci gaban kowacce kasa.
Ya ce a shirye kasar Sin ta ke, ta hada hannu a fannin kiwon lafiya da shirin hukumar WHO na shekaru 5 masu zuwa, karkashin shirinta na "Ziri daya da hanya daya", da kuma tsarin hadin gwiwar kasar Sin da Afrika da kuma burinta na samar da al'umma mai matsakaiciyar ci gaba ta kowacce fuska kamar yadda yake kunshe cikin burika 2 da take son cimmawa yayin da take bikin shekaru 100 guda 2, da nufin taimakawa ci gaban kiwon lafiya a duniya da amfanawa zuri'a na gaba.
A nasa bangaren, Shugaban na WHO, ya bayyana godiyarsa ga taimakon da kasar Sin ke ci gaba da bayarwa ga harkar kiwon lafiya a duniya, da kuma kudurin WHO na shiga cikin shawarar "Ziri daya da Hanya daya". (Fa'iza Mustapha)