in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Idan Amurka ba ta canza matakan da yake dauka bisa radin kai ba, ganawa tsakanin Trump da Putin ba za ta iya dawo da huldar dake tsakanin kasashen Amurka da Rasha ba
2018-07-17 21:47:33 cri
A jiya ne, shugaban kasar Amurka Donald Trump da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin suka yi ganawa ta farko a birnin Helsinki na kasar Finland. Bayan da suka shafe wasu sa'o'i suna tattaunawa a asirce a fadar shugaban kasar Finland, sun kuma bayyana cewa, ganawar farko da suka yi tana da "ma'ana sosai".

Dalilin da ya sa Trump ya tsaya kan ra'ayinsa na ganawa da Mr Putin shi ne, ya yi la'akari sosai a wasu fannoni: da farko, yana son samar da wani kyakkyawan yanayi domin zaben da za a yi a watan Nuwamban bana a kasar Amurka. Sannan yana son matsa wa kasashe mambobin kungyar NATO bisa karfin Putin, ta yadda kasar Amurka za ta samu wasu kyawawan sharuda kan kudaden da ake amfani da su a kungiyar NATO.

A bangaren shugaba Putin, kowane irin sakamako zai bullo, ganawa tsakaninsa da Donald Trump wani muhimmin mataki ne ga manufofin diflomasiyyar kasar Rasha na bana.

A yayin da huldar dake tsakanin Rasha da kasashen yammacin duniya ta shiga wani mummunan hali sakamakon rikicin Ukrain, ganawa tsakanin Rasha da Amurka ta zama wani gwaji da bangaren Rasha ya yi domin kokarin kawo karshen irin wannan mawuyacin hali. Sabo da haka, Mr. Putin ya mai da hankalinsa, har ma ya sa rai kan wannan ganawa.

A hakika, dangantakar dake tsakanin kasashen Rasha da Amurka na da sarkakiya matuka, manyan sabanin dake a tsakaninsu guda biyu ne, wato rikici kan moriya, sannan rikici kan tunaninsu game da duniyarmu.

Duk da sabanin dake tsakanin Rasha da Amurka kan batun Syria, amma bangarorin biyu suna iya yin shawarwari kan batun. Kana, sabanin dake tsakanin bangarorin biyu kan batun Ukraine batu ne na tarihi, a ganin kasar Rasha, maido da yankin Crimea bukatun al'ummar kasarta ne a fannin kiyaye tsaron kasa, a ganin kasar Amurka kuwa, yakin da bai cancanta ba, lamarin ya kawo barazana ga kokarin kare tsaron kasashen Turai. Game da wannan batu, Rasha da Amurka sun kasa cimma matsaya a kai

A halin yanzu, idan ana son kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu, ya kamata a warware manyan batutuwan da suka kawo sabani a tsakaninsu, baya ga yanayin siyasa maras kyau da Amurka ta nuna wa kasar Rasha. Idan kasar Amurka ta ci gaba da dagewa a kan matsayin da ta dauka a halin yanzu, tabbas, babu wanda zai iya cimma nasara kan batun kyautata huldar dake tsakaninta da kasar Rasha. (Sanusi Chen, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China