in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa karo na 20 tsakanin shugabannin Sin da Turai
2018-07-17 13:40:17 cri
<
P>An kaddamar da taro karo na 20 tsakanin shugabannin kasar Sin da kasashen Turai Jiya Litinin a nan birnin Beijing, karkashin jagorancin firayin ministan kasar Sin Li Keqiang da shugaban majalisar kasashen Turai Donald Tusk da shugaban hukumar tarayyar kasashen Turai Jean Claud Juncker, inda sassan biyu suka cimma matsaya guda kan batun kiyaye tsarin kasa da kasa bisa tushen ka'idojin da aka tsara, tare kuma da nuna goyon baya ga harkar gudanar da cinikayya tsakanin bangarori da dama da cinikayya maras shinge. Haka kuma, sassan biyu sun tsai da kuduri cewa, za su kafa tsarin kungiyar aiki domin tattauna batun yin kwaskwarima a hukumar cinikayya ta duniya.

A halin da ake ciki yanzu, yanayin da kasashen duniya ke ciki yana da sarkakiya, a don haka taron ganawar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai da aka gudanar a nan birnin Beijing ya jawo hankalin kafofin watsa labarai na kasa da kasa matuka.

Yayin ganawar, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, cudanya da hadin gwiwa dake tsakanin kasarsa da kasashen Turai tana da muhimmanci matuka, saboda sassan biyu suna taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arzikin duniya, kana kokarin da sassan biyu su ke yi wajen gudanar da cinikayya tsakanin bangarori da dama da cinikayya maras shinge zai kawo tasiri ga ci gaban tattalin arziki a fadin duniya, yana mai cewa, "Yayin da muke tattaunawa a tsakaninmu, gaba daya mun amince cewa, a halin da ake ciki yanzu, kamata ya yi mu yi kokari tare domin kiyaye tsarin gudanar da cinikayya dake tsakanin bangarori da dama, da haka za a cimma burin tabbatar da tsarin demokuradiyar siyasa da kiyaye zaman lafiya a fadin kasashen duniya. kana kamata ya yi mu yi kokari tare domin kiyaye cinikayya maras shinge, a karshe dai za mu sa kaimi kan farfadowar tattalin arzikin duniya."

Li Keqiang ya kara da cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasashen Turai domin kara karfafa cudanya da hadin gwiwa dake tsakaninsu, haka kuma za su iya ingiza huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninsu yadda ya kamata.

Yayin taron, sassan biyu sun amince cewa, za su yi kokarin kiyaye ka'idojin MDD da dokokin kasa da kasa, kuma za su kara karfafa cudanyar dake tsakaninsu a fannonin harkokin diplomasiyya da samar da tsaro, tare kuma da adawa da manufar ba da kariya ga cinikayya da gudanar da cinikayya bisa kashin kai. Ban da haka, sassan biyu sun tsai da kuduri cewa, za su kafa tsarin kungiyar aiki domin tattauna batun yin kwaskwarima a hukumar cinikayya ta duniya.

Kana yayin taron ganawar, sassan biyu sun gabatar da jerin kayayyakin da gwamnatocin kasashen za su yi sayayya tsakaninsu bisa shawarwari kan yarjejeniyar zuba jari, inda Li Keqiang ya yi nuni da cewa, "Kasar Sin da kasashen Turai sun riga sun cimma matsaya guda kan jerin kayayyakin da gwamnatocin kasashen za su sayayya bisa shawarwari kan yarjejeniyar zuba jari, wannan na alamta cewa, shawarwari kan yarjejeniyar zuba jarin da sassan biyu suka yi a cikin shekaru hudu da suka gabata, ya samu sabon ci gaba, wato ya riga ya shiga mataki mai muhimmanci, kuma tabbas zai sa kaimi kan shawarwarin dake tsakaninsu, nan gaba kuma za su ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar wurin samar da kayayyaki tsakaninsu kafin karshen watan Oktoban bana, lamarin zai taimakawa cinikayyar kayayyakin aikin gona tsakaninsu. Nan gaba kasar Sin za ta kara karfafa huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninta da kasashen Turai, abu mafi muhimmanci shi ne kasar Sin ta riga ta bude kofarta, kuma za ta kara bude kofarta a nan gaba."

Kazalika, sassan biyu su ma sun yi alkawari cewa, za su kara karfafa cudanya wajen kiyaye ikon mallakar fasaha, da bude kofa ga juna, tare kuma da kara kyautata kasuwa da muhallin zuba jari ga juna.

Shugaban majalisar kasashen Turai Donald Tusk da shugaban kwamitin tarayyar kasashen Turai Jean Claud Juncker su ma sun bayyana cewa, kasashen Turai suna farin cikin ganin ci gaban da kasar Sin ta samu, haka kuma suna farin cikin ganin muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a cikin harkokin kasa da kasar, yanzu huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai tana da muhimmanci matuka, shugaban kwamitin tarayyar kasashen Turai Jean Claud Juncker yana mai cewa, "Har kullum ina cike da imani kan karfi da sirrin ci gaban huldar hadin gwiwar dake tsakanin tarayyar Turai da kasar Sin, ko shakka babu huldar dake tsakaninmu tana da muhimmanci matuka, musamman ma a halin da ake ciki yanzu, saboda tarayyar Turai ta kai sahun gaba wajen gudanar da cinikayya da kasar Sin, kasar Sin ita ma ta kasance matsayi na biyu wajen cinikayya da tarayyar Turai."

A nata bangare, tarayyar Turai ta bayyana cewa, tana son yin kokari tare da kasar Sin domin ciyar da huldar abota bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninsu gaba yadda ya kamata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China