in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ki amincewa da zargin da kasar Amurka ta yi wai ta dade tana cinikin rashin adalci
2018-07-16 19:40:36 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yayin taron manema labarun da aka gudanar a yau Litinin cewa, Sin ta yi watsi da zargin da kasar Amurka ta yi a cikin sanarwar bincike mai lamba 301 cewar wai Sin ta dade tana rashin adalci a harkokinta na ciniki. Hua Chunying ta yi nuni da cewa, zargin da kasar Amurka ta yi ba shi da tushe kuma babu gaskiya a cikinsa.

Hua Chunying ta yi nuni da cewa, rashin daidaito a kan ciniki bai yi daidai da rashin adalci ba. An tsara ka'idojin kasa da kasa ta hanyar yin shawarwari don samun adalci, ba wani ne ya fada ko ya tsara ma'auni da kansa, har ya amfana ta hanyar kawo illa ga muradun sauran kasashen duniya ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China