in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta bukaci kasashen Turai da su ba ta tabbaci game da yarjejeniyar nukiliyar ta
2018-07-16 13:25:51 cri

Shugaban addini na kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kira ga kasashen Turai da su bayyanawa kasar sa hakikanin matsayin su, game da aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma.

Khamenei ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi, yana mai cewa, dole ne kasar sa ta dauki wasu sahihan matakai na raya tattalin arzikin ta, maimakon dogaro da yarjejeniyar nukiliya, wadda aka yiwa lakabi da JCPOA.

A ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata ne dai shugaban Amurka Donald Trump, ya ayyana ficewar kasar sa daga yarjejeniyar, tare da aniyar sa ta mayarwa Iran din takunkumin da a baya Amurkar ta dage mata, wanda ya shafi gurgunta tattalin arzikin kasar a matakan koli.

Bisa yarjejeniyar JCPOA, Iran za ta yiwa kan ta kaidi game da sarrafa makamashin nukiliya, a hannu guda kuma za a dage mata takunkumin da kasashen duniya suka kakaba mata.

Tun bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar, kasashen Turai na ta daukar matakan ganin Iran ta amfana daga moriyar tattalin arziki a sassa daban daban, domin tabbatar da dorewar biyayyar ta ga tanaje tanajen yarjejeniyar, yayin da kasashen na Turai ke fatan cika alkawarun da suka dauka kan batun.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China