in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan GDPn farkon rabin shekarar bana na kasar Sin ya karu da kashi 6.8 cikin dari
2018-07-16 10:49:16 cri
Hukumar kididdigar ta kasar Sin ta ba da wani rahoto cewa, yawan GDPn farkon rabin shekarar bana na kasar ya kai RMB bilyan 41896.1, wanda ya karu da kashi 6.8 bisa dari na makamancin lokaci na bara.

Wannan alkaluma dai sun bayyana cewa, yawansa GDPn ya karu da kashi 6.8 cikin dari a farkon watanni uku na bana, inda a watanni Afrilu, Mayu da Yuni ya karu da kashi 6.7 cikin dari, inda ya samun karuwa daga kashi 6.7 zuwa 6.9 cikin dari cikin watanni 36 a jere.

Kakakin hukumar Mao Shengyong ya bayyana a wani taron manema labaru cewa, tattalin arzikin al'ummar Sin ya samun bunkasuwa yadda ya kamata cikin karko a farkon rabin shekara, inda aka gudanar da kyautatuwa kan tsare-tsare masu zurfi, da sauyin karfin bunkasuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata. Kana an samun riba da bunkasuwa mai inganci bisa tsarin da aka aiwatar. (Amina Xu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China