in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNESCO tana fatan daga matsayin dangantakarta da Sin zuwa matsayin koli
2018-07-16 10:41:51 cri

Kasar Sin, wadda ta rungumi harkokin gamayyar kasa da kasa, babbar abokiyar hadin gwiwar hukumar UNESCO ce, "za mu karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da UNESCO, kuma za mu daga matsayin alakar zuwa matsayin koli", in ji Audrey Azoulay, babbar daraktar hukumar UNESCO.

Tun daga ranar yau 16 zuwa 19 ga watan nan na Yuli, Azoulay za ta kai ziyararta ta farko zuwa kasar Sin a matsayinta na babbar daraktar hukumar kula da ilmin kimiyya da raya al'adu ta MDD wato (UNESCO).

Azoulay, wacce tsohuwar ministar raya al'adun kasar Faransa ce, ta karbi ikon tafiyar da hukumar ne a watan Nuwambar bara a matsayin babbar jami'ar hukumar MDDr na tsawon shekaru 4.

Audrey Azoulay, wadda ta sha kai ziyara a kasar Sin a lokuta da dama cikin shekaru sama da 10, ta ce ta yi farin ciki matuka da yadda kasar Sin ta samu bunkasuwa.

Ta ce, "Idan muka duba yadda matsayin ilmi yake, akwai gagarumin ci gaba da aka samu tun daga shekarun 1980s, kuma gibin dake tsakanin maza da mata ta fuskar ilmi ya yi matukar raguwa a cikin shekaru 20. Wannan shi ne irin nasarar ci gaban tattalin arzikin da kasar Sin ta samu da kuma ci gaban da ta samu a fannin fasahohi."

Ta kara da cewa, kasar Sin tana daya daga cikin muhimman kasashen duniya da suke kokarin kiyaye tarihin al'adu ta hanyar bin ka'idojin hukumar UNESCO.

Azoulay ta ce, UNESCO da Sin suna da kyakkyawan hadin gwiwa a fannoni da dama, da suka hada da daga matsayin ilmin mata da yara mata, horas da kwararru daga kasashen Afrika da sauransu. A cewarta, "A bisa ga irin nasarorin da aka riga aka cimma, za mu iya daga matsayin dangantakarmu zuwa matsayin koli."(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China