in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Wane irin makomar da ra'ayin kama karya kan fasahohi na kasar Amurka zai samu
2018-07-14 17:10:02 cri

Amurka kasa ce mafi karfi a fannin kimiyya da fasaha a duniya, kuma ta zama ja gaba wajen yin kirkire-kirkire a wannan fanni. Amma a kwanakin baya, Amurka ta yi amfani da rikicin ciniki wajen daukar matakai don kayyade mu'amala da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin a fannin kimiyya da fasaha, kana ta gabatar da rahoto mai taken "yadda harin tattalin arziki na kasar Sin ya kawo barazana ga ikon mallakar fasahohi da ilmi na kasar Amurka da ma duniya baki daya", daga baya Amurka ta zartas da dokar kayyade kamfanonin kasashen waje da suka zuba jari ga kasar, har ma ta hana wasu kasashe samun muhimman fasahohi daga wajenta, wannan alama ce ta ra'ayin kama karya kan fasahohi na kasar Amurka.

A halin yanzu, ra'ayin kama karya kan fasahohi na kasar Amurka ya yi shafi a fannoni hudu. Na farko, ta yi amfani da hana muhimman fasahohi wajen yaki da 'yan takararta don samun babbar riba. Na biyu, ta tsoma baki kan ayyukan takara na kasuwanni bisa dalilin tabbatar da tsaron kasar, da bada kariya ga muhimman fasahohi da kasuwarta, da kawo illa ga ka'idojin kasuwa da zuba jari. Na uku kuwa, ta kayyadewa wasu kasashe shigar da kayayyakin fasahohin zamani kasarta ta hanyar daga harajin kwastam, don hana bunkasuwar sha'anin fasahohin zamani a sauran kasashen duniya.

Abin bakin ciki shi ne, gwamnatin kasar Amurka ta yi la'akari da tattalin arziki da zamantakewar al'ummarta, ta dauki matakai don kayyade fitar da fasahohi zuwa sauran kasashen duniya da hana bunkasuwar fasahohin sauran kasashe, hana bunkasuwar sauran kasashe ta hanyar fasahohi don cimma burinta, hakika dai, wannan shi ne ra'ayin kama karya kan fasahohi, kuma babu shakka za a samu mugun sakamako a nan gaba.

Na farko, aikin bin ra'ayin kama karya kan fasahohi zai haddasa rikicin fasahohi da ciniki na duniya, wanda zai kawo babbar illa ga bunkasuwar fasahohin duniya da tattalin arzikin kasa da kasa, watakila zai haddasa koma bayan tattalin arzikin duniya, da kawo cikas ga farfado da tattalin arzikin duniya bayan rikicin hada-hadar kudi.

Na biyu, ta yi watsi da tsarin rarraba aiki na duniya da ka'idojin kasa da kasa, inda ta dauki matakai bisa ra'ayin kanta, abun da zai kawo illa ga tsarin rarraba aiki na duniya, da sabawa ka'idojin kasa da kasa, a karshe dai ba zai haifar da moriya ko kadan ba.

Na uku, ba ta girmama bukatun bunkasuwar fasahohi na sauran kasashen duniya ba, sauran kasashen duniya ba za su nuna goyon baya gare ta ba.

Na hudu, ta yi watsi da bukatun bude kofa ga kasashen waje a fannin bunkasa fasahohi, da hana bunkasuwar fasahohi, don haka ba za ta yi kokarin yin takara da sauran kasashen a fannin kimiyya da fasaha ba, a karshe dai, wannan ba zai bunkasa fasahohin ta ba.

Babu shakka, ba za a canja tsarin raya tattalin arzikin duniya na bai daya ba, ana bukatar yin kwaskwarima kan sarrafa duniya bisa tsarin bai daya, ra'ayin kama karya daga bangare daya ya sabawa bukatun bunkasuwar kasa da kasa har ma da na duniya, ba za a samu kyakkyawan sakamako ba. Ya kamata a ci gaba da bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa, da samun bunkasuwa ta hanyar bude kofa, da sa kaimi ga hadin gwiwa a fannonin samar da kayayyaki da sana'o'i da yin kirkire-kirkire, da bunkasa kimiyya da fasaha da tattalin arziki a duniya baki daya, wannan shi ne zabi mafi dacewa. Duk wani aiki na ra'ayin kama karya kan fasahohi da sabawa ka'idojin tattalin arziki da kimiyya da fasaha, ba za su haifar da da mai ido ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China