in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da takwararsa ta Botswana
2018-07-14 15:30:52 cri

Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da ministar harkokin waje da hadin gwiwa ta kasar Botswana, Unity Dow, wadda ke ziyara a kasar Sin.

Wang Yi ya bayyana cewa, taron kolin dandalin hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da za a shirya a nan birnin Beijing cikin watan Satumban dake tafe, na da babbar ma'ana ga ci gaban huldar dake tsakanin sassan biyu wato Sin da Afirka. Ya ce, gwamnatin kasar Sin na maraba da kasar ta Botswana, da ta shiga shawarar ziri daya da hanya daya, haka kuma tana maraba ga kasar da ta halarci bikin kasa da kasa, na baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su daga ketare, na kasar Sin karo na farko, wanda za a yi a watan Nuwamban bana a birnin Shanghai dake kudancin kasar.

A nata bangare, Unity Dow ta bayyana cewa, shugaban kasarta Mokgweetsi Masisi da gwamnatin kasar sun amince da manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma suna goyon bayan tunanin shugaba Xi Jinping game da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil Adama da kuma shawarar ziri daya da hanya daya. Ta ce har kullum, kasar Botswana tana kiyaye tsarin gudanar da cinikayya tsakanin bangarori da dama.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China