in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar tashin bam a Pakistan ya karu zuwa 128
2018-07-14 15:19:46 cri

Adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar bam a wani wurin gangamin siyasa a yankin Mastung na lardin Balochistan dake kudu maso yammacin kasar Pakistan ya karu zuwa 128 ya zuwa safiyar yau Asabar.

Da yake tabbatar da adadin, minista mai kula da lardin Balochistan, Agha Umar, ya ce sama da mutune 120 ne suka raunana sanadiyyar harin.

Kakakin gwamnatin lardin, ya sanar da ayyana kwanaki biyu na makoki yayin da za a yi kasa da tutocin kasar zuwa rabin sanda a gine-ginen gwamnati.

Shi kuwa mataimakin kwamishinan yankin Mastung, Qaim Lashari, cewa ya yi an yi niyyar kai harin ne kan 'dan siyasa Nawabzada Siraj Raisani, wanda ke halartar gangamin siyasa a mazabarsa.

An garzaya da 'dan siyasar da ya yi rashin matashin dan sa a shekarar 2011 saboda ayyukan 'yan ta'adda, zuwa asibiti dake Quetta, babban birnin lardin, bayan ya samu raunuka.

Kungiyar IS dai ta dauki alhakin kai wannan hari a shafinta na yanar gizo.

Shugaban kasar Mamnoon Hussain da mai rikon mukamin firaministan kasar Nasir-ul-Mulk da shugaban rundunar sojin kasar Qamar Javed Bajwa sun yi tir da harin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China