in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Sin ya gana da ministar wajen Botswana
2018-07-13 19:54:03 cri

Mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan, ya gana da ministar harkokin waje da hadin gwiwar kasashe ta Botswana Unity Dow a Juma'ar nan, inda ya bayyana bukatar kasashen biyu, su karfafa amincewa juna ta fuskar siyasa, su fadada hadin gwiwa a dukkanin fannoni, tare kuma da cimma gajiyar ci gaban su tare.

Wang Qishan ya jinjinawa dadadden kawance mai cike da moriya dake wanzuwa tsakanin sassan biyu, yana mai fatan za a kai ga shigar da fatan nan na samar da "al'ummar duniya mai makoma guda" cikin tsarin alaka da mu'amalar Sin da kasashen nahiyar Afirka.

A nata bangaren uwargida Dow ta bayyana cewa, kasar ta na dora muhimmancin gaske game da alakar ta da kasar Sin, tana kuma kan bakar ta ta amincewa da wanzuwar kasar Sin daya tak a duniya.

Kaza lika jami'ar ta bayyanawa Mr. Wang cewa, shugaban kasar Botswana Masisi, na fatan zuwan lokacin taren FOCAC wanda birnin Beijing zai karbi bakunci, domin karfafa zumunci, da alakar dake akwai tsakanin daukacin nahiyar Afirka da Sin, karkashin lemar shawarar nan ta ziri daya da hanya daya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China