Wannan matakin ya biyo bayan dabarar da gwamnati ta dauka na daukaka zaman lafiya da aiwatar da sakamakon taron tattaunawar batutuwan kasa.
Cikin shekarun da suka gabata, Gwamnati da bangaren dake adawa da ita sun ci gaba da sabunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yankunan dake fama da rikici.
A watan Yunin 2016 ne, shugaba al-Bashir ya fara ayyana tsagaita bude wuta da watanni hudu, domin ba 'yan tawaye damar halartar taron tattauna batutuwan kasa. Tun daga wancan lokaci ne kuma ake ta tsawaita yarjejeniyar. (Fa'iza Mustapha)