in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kayayyakin shige da fice na kasar Sin ya kai yuan biliyan 14,120
2018-07-13 13:25:30 cri
Kakakin hukumar kwastan ta kasar Sin Huang Songping ya bayyana cewa, a farkon rabin shekarar da muke ciki, yawan kayayyakin shige da fice na kasar Sin a cinikayyar da ta yi da kasashen ketare, ya kai kudinta Yuan biliyan dubu 14 da 120, adadin da ya karu da kashi 7.9%, a kwatankwacin makamancin lokacin shekarar bara. Ya ce daga cikinsu, yawan kayayyakin da ta fitar zuwa kasashen waje ya kai yuan biliyan 7510, adadin da ya karu da kaso 4.9%, a yayin da adadin kayayyakin da ta shigo da su daga kasashen waje ya kai yuan biliyan 6610, adadin da ya karu da kashi 11.5%. Kana rarar kudin ciniki kuma ta kai yuan biliyan 901.32.

Kakakin wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya kira a yau Jumma'a ya ce, cinikayyar shige da fice da kasar Sin ta yi da kasashen ketare ta gudana yadda ya kamata a farkon rabin wannan shekara, ta kuma ta kyautata tsarinta da ingancinta.

Sai dai a cewarsa, a yayin da ake kara fuskantar rashin tabbas a duniya, kasar Sin za ta fuskanci wasu kalubaloli a cinikayyarta da kasashen ketare. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China