Powell ya fadi haka ne yayin da yake hira da manema labaru, inda ya ce sauyawar manufar ciniki ta kasar Amurka ta sanya karin damuwa a zukatan kamfanonin kasar, sai dai har zuwa yanzu an kasa hasashen matakin da gwamnatin kasar za ta dauka a nan gaba.
A ganin jami'in na Amurka, idan matakin da kasar ta dauka a fannin cinikayya ta sa harajin kwastam ya ragu, to, zai amfanawa tattalin atzikin kasar. Amma idan manufar cinikin kasar ta kara harajin kwastam mai yawa kan kayayyaki daban daban, sa'an nan za a aiwatar da wannan manufa cikin dogon lokaci mai zuwa, to, mai yiwuwa lamarin ya raunana tattalin arzikin kasar. (Bello Wang)