in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abin gaskiya daya kadai na kasancewa kan cinikayyar da ake yi tsakanin kasar Sin da ta Amurka
2018-07-13 12:13:37 cri

Amurka ta fitar da rahoton bincike mai lamba 301 a matsayin hujjar ta da yakin ciniki da kasar Sin a 'yan watannin baya. A ran 10 ga wata ne, ofishin kula da harkokin ciniki na Amurka ya ba da wata sanarwa dangane da wannan rahoto, inda ta zargi kasar Sin da gudanar da ciniki maras adalci ba gaira ba dalili. Alkaluma da dalilai da aka bayar a wannan rahoto, babu kamshin gaskiya a cikinsu ko kadan.

Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta ba da wata sanarwa a jiya Alhamis don karyata jita-jitar da Amurka take yi cikin rahoton, ciki hadda wai babu daidaito a cinikayyar Sin da Amurka, kwace 'yancin mallakar fasaha, tilastawa sauran kasashe samar da fasahohin zamani ga kasar Sin, da shirin samar da kayayyaki kirar kasar Sin nan da shekarar 2025 da dai sauransu.

Da farko, za mu duba gibin ciniki tsakanin kasashen biyu. Ma'aikatar cinikayya ta Sin ta bayyana cewa, dalilai uku da suka haddasa wannan batu su ne, Amurka ba ta da isashen kudaden ajiya a bankunan gida, da kuma kudinta dala a matsayin kudin da aka adanawa a duk duniya, kana Amurka ta kayyade fitar da kayayyakin fasahohin zamani bisa tunaninta na yakin cacar baki.

Na biyu, Amurka ta yi tir da yadda kasar Sin ta kwace 'yancin mallakar fasaha, wannan zargi ba shi da wata hujja. Ya zuwa yanzu, Sin ta aiwatar da matakan kare 'yancin mallakar fasaha a wasu manyan fannoni ciki hadda 'yancin mawallafi, tambura, alamomin mallakar, martaba sirrin kasuwa, sabbin nau'o'in tsire-tsire da dai sauransu, wannan ya taimaka wajen samar da tsari mai inganci wajen kare 'yancin mallakar fasaha ta fuskokin doka, ka'ida da sauransu. Ban da wannan kuma, Sin ta kafa kotuna ko hukumomin kare 'yancin mallakar fasaha a biranen Beijing, Shanghai, Guangzhou da sauranu wurare, har ma an yi wa hukumar dake kulawa da 'yancin mallakar fasaha ta Sin garambawul, matakin da ya baiwa kamfanonin kasashen waje da dama zarafin kai kara kan wannan batu a kasar Sin, alal misali, kamfanonin samar da takalmai 3 na kasar Sin sun keta tambarin kamfanin New Balance, hakan ya sa kotun Sin ta yanke musu hukuncin biyan kudin fansa RMB miliyan 10, kudade mafi yawa da kamfanonin ketare suka samu a nan kasar Sin sakamakon keta hakkin tambarinsu.

Na uku, game da batun tilastawa sauran kasashe su samar da fasahohin zamani ga kasar Sin, wani labarin jabu. Sin ta ba fitar da ko wata doka ko manufa ko guda don ta tilasta wa kamfanonin ketare da su samar da fasahohin zamani nasu ga kasar Sin idan sun zuba jari a nan kasar Sin.

A cikin shekaru 40 da suka gabata, Sin ba ta sa hannu kan ko yarjejeniyar tilastawa kamfanonin ketare da su samar da fasahohin zamani nasu ga kasar Sin ko guda ba, kuma babu wani kamfanin ketare da ya kai kara kan wannan batu. Ko shakka babu, Sin ba ta taba mai da wannan batu a matsayin sharadin da tilas a bi don shiga kasuwannin kasar Sin ba.

Na karshe, game da zargin da Amurka ta yi wa shirin "Samar da kayayyaki kirar kasar Sin nan da shekarar 2025" da Sin ta gabatar. An nuna cewa, Amurka ta gabatar da wannan rahoto ne da niyyar hana aiwatar da shirin samar da kayayyaki bisa sabbin fasahohin zamani da kasar Sin take yi, ta yadda za ta hana bunkasuwar Sin. Amurka tana da shirinta na abotar samar da kayayyaki na zamani, Jamus na da shirin bunkasa masana'antu na kashi na 4, don me Sin ba ta da ikon fitar da shirinta na raya masana'antun samar da kayayyakin dake kunshe da fasahohin zamani ba?

Idan aka yi maganar manufar samar da tallafin kudi, gwamnatin Amurka ma tana samarwa kowace cibiyar dake yin aikin kirkire-kirkire ta kasar tallafin kudi dala miliyan 5 a kowace shekara tun daga shekarar 2015 zuwa ta 2024. Idan gwamnatin Amurka ba ta baiwa wadannan kamfanoni tallafin kudi a fannonin gonakin da suke amfani da su, harajin kwastam, ba da rancen kudi, samar da kayayyakin yau da kullum, nuna goyo bayan ayyukan kirkire-kirkire da dai sauransu, Silicon Valley ba zai taso har ya samu wadata kamar haka ba.

"Samar da kayayyaki kirar kasar Sin nan da shekarar 2025" wani shiri ne dake mayar da hankali ga samun bunkasuwa bisa tsarin kasuwanci dake bude kofa ga masu ruwa da tsaki, gwamnatin kasar Sin ta dauki nauyin ba da jagoranci ne kawai. Shugabannin kasar Sin sun sha jaddadawa cewa, wannan shiri yana maraba da kamfanonin kasashen waje, yanzu haka kamfanoni daga Amurka, Jamus, Birtaniya da sauransu sun zo kasar Sin bisa wannan shiri.

Muna iya ganin cewa, Amurka ba ta dauki ma'auni irin daya kan kasar Sin ba da zummar hana bunkasuwar sha'anin samar da kayayyaki na zamani na kasar Sin. Matakin da ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka ba ta da karfin daidaita matsalolin da take fuskanta a cikin gida. Kuma bunkasuwar kasar Sin na ta da hankalinta kwarai da gaske, abin da ya sa Amurka ta dauki tunanin yin watsi da hadin kai da zummar tinkarar abokiyar takararta.

Abu mai ban sha'awa shi ne, rahoton da Amurka ta fitar ya gabatar da wasu shaidu ne da suka samu amincewar bangaren gwamnatin Amurka da kamfanoninta kawai, har ma ta yi amfani da kalmomin "na ji an ce" ko "masu ruwa da tsaki suna tsamanin cewa", lalle wadannan abubuwa ba su da tushe ko kadan, wa zai yarda da ita? (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China