in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tabbas kasar Sin za ta yi galaba a yakin cinikayya
2018-07-12 19:30:19 cri

Tun lokacin da fadar White House ta kasar Amurka ta kaddamar da yakin cinikayya da kasar Sin, daya bayan daya wasu manyan mutane a kasar, kamar su tsohon shugaban asusun ko ta kwana na tarayyar Amurka Alan Greenspan, da Paul Krugman, wanda ya taba samun lambar yabo ta Nobel kan ilmin tattalin arziki, sun zargi manufar shugaba Trump, suna masu cewa, matakin zai lahanta moriyar al'ummun kasar ta Amurka, haka kuma zai yi tasiri ga ci gaban tattalin arzikin kasar, amma fadar White House ta kasa kula da hakan, har ma ta sanar da aniyar kasar ta kara kudaden haraji har kaso 10 bisa dari, a kan jerin kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa Amurka, wadanda adadin kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 200.

A halin da ake ciki yanzu, majalisar dattijai ta kasar ta zartas da wani kuduri bisa kuri'un mafiya rinjaye, inda aka bukaci idan har Mr. Trump na son kara kudaden haraji kan kayayyakin ketare, to dole ne ya samu amincewa daga wajen majalisar dokokin kasar.

Amma kasar Sin tana gudanar da aiki bisa matakai daban daban, saboda ta fahimci cewa, muddin dai ta gudanar da aikinta yadda ya kamata, hakan zai ba ta damar yin nasara a yakin cinikayyar da Amurka ta kaddamar.

Aiki mafi muhimmanci dake gaban gwamnatin kasar Sin shi ne raya tattalin arziki mai inganci, tare kuma da biyan bukatun al'ummun kasar. A sa'i daya kuma, ta taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin kasashen duniya bisa matsayinta na babbar kasa, daga karshe kuma ta gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama.

Hakika yakin ciniyayya zai yi tasiri ga ci gaban kasar Sin cikin gajeren lokaci, amma idan an yi hangen nesa, za a gano cewa, yakin cinikayya zai amfani ci gaban kasar ta Sin.

Da farko dai, masana'antun kasar Sin sun samu ci gaba cikin sauri, kana tana da babbar kasuwa wadda ke da masu sayayya da yawansu ya kai biliyan 1 da miliyan 400, hakan ya nuna cewa, kasar Sin tana iya samar da kusan daukacin kayayyaki, haka kuma tana iya sayar da su a cikin gidan ta.

Na biyu, bukatun al'ummun kasar a cikin gida sun sa kaimi kan ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin, inda a yanzu aka cimma burin karuwar tattalin arziki da kaso 91 bisa dari bisa bukatun gida.

Na uku, kasar Sin ta samu ci gaba a bayyane wajen kirkire-kirkire. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, adadin kamfanonin kirkire-kirkiren kasar Sin ya kai matsayi na biyu a fadin duniya, kana rahoton huhumar ikon mallakar fasaha ta duniya ya nuna cewa, kasar Sin ta riga ta shiga jerin kasashe 20 wadanda suka fi karfi a fannin kirkire-kirkire.

Na hudu, manufar bude kofa ta kasar Sin tana samar da moriyar ci gabanta ga sauran kasashen duniya.

Rahoton binciken muhallin kasuwancin kasar Sin a shekarar 2018, na kungiyar kamfanonin kasar Amurka dake kasar Sin ya nuna cewa, kamfanonin kungiyar kaso 74 bisa dari za su kara zuba jari a kasar Sin, adadin da ya kai matsayin koli a cikin shekarun bayan bayan nan.

Mataimakin shugaban asusun IMF na farko David Lipton ya bayyana cewa, yana cike da imani kan kasar Sin, cewa za ta kyautata tsarin tattalin arziki, tare kuma da cimma burin dauwawammen ci gaban tattalin arzikin ta. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China