in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karin kamfanonin kasar Amurka na zuwa kasar Sin don neman hadin gwiwa yayin da fadar White House ke kara matsa wa kasar Sin lamba ta fannin cinikayya
2018-07-12 11:58:42 cri





Cikin kusan mako guda da kasar Amurka ta tada yakin cinikayya, al'amuran da suka faru biyo bayan yakin sun jawo hankalin al'umma. 

A ranar 10 ga wata da dare, agogon gabashin kasar Amurka, ofishin kula da harkokin cinikayyar kasar Amurka ya bayyana karin wasu kayayyakin kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 200 wadanda za a kara sanya musu harajin da ya kai kashi 10%, bisa dalilin wai "kasar Sin ta mayar da martani kuma ba ta gyara wasu matakanta a fannin ciniki ba". A game da wannan, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana cewa, yadda Amurka ta gaggauta fitar da jerin kayayyakin da za ta kara sanya musu haraji, abu ne da ba za a yarda da shi ba, kuma "domin kiyaye muradun kasar da na al'ummarta, gwamnatin kasar Sin ba ta da wani zabi illa ta mayar da martanin da ya dace".

A hakika, daga kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 50 zuwa biliyan 200, idan da gaske ne Amurka ta sanya haraji kan gaba dayan kayayyakin nan da ta bayyana, lalle ta rufe kofarta ga fiye da rabin kayayyakin kasar Sin dake shiga cikin kasarta. Alkaluman kididdiga da hukumar kwastan ta kasar Sin ta fitar na nuna cewa, darajar kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa kasar Amurka a shekarar 2017 ta kai dala biliyan 429 da miliyan 800. Ke nan idan masu sayayya na kasar Amurka sun sayi kayayyakin da aka bayyana, lalle za su kara biyan kudi a kalla kaso 10%. Don haka ne, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta yi suka cewa, wannan "mataki na rashin hankali da Amurka ta dauka ba zai samu karbuwa a wajen jama'a ba", kuma "ya kawo barna ga kasar Sin da duniya baki daya, har da kanta".

Amma ko ma da gaske ne gwamnatin Trump tana da wannan niyya, kuma idan ta kare aniyarta, yaya za ta kai ga cimma burinta na "sake daukaka kasar Amurka a duniya"? Don haka, fadar White house ta fitar da takardar jerin kayayyakin ne da nufin matsa wa kasar Sin matuka, ta yadda za ta hana ta mai da martani tare da mika wuya ga Amurka. Za a shafe kimanin watanni biyu ana sauraron ra'ayoyin al'umma game da jerin kayayyakin da aka bayyana, don haka, za a ci gaba da fuskantar rashin tabbas.

Amma duk sakamakon da ya biyo baya, a game da batutuwan da suka shafi muradun kasa da na al'umma, duk wata kasa mai 'yanci ba za ta ba da kai ba. Don haka, tabbas kasar Sin za ta dauki matakai na mayar da martani. Abu mai sha'awa shi ne, karin kamfanonin kasar Amurka da al'ummarta sun fara nuna adawarsu a yayin da illolin da yakin cinikayya da White House ta tayar ke kara karuwa. A cikin kwanakin baya ne, jama'a daga bangarorin siyasa da kasuwanci na kasar Amurka sun zo nan kasar Sin don neman hadin gwiwa mai dorewa.

A ranar 10 ga wata, kamfanin Tesla na kasar Amurka da ya shahara wajen kera motoci masu aiki da wutar lantarki ya daddale yarjejeniyar zuba jari a fannin kera motoci masu aiki da wutar lantarki a birnin Shanghai, wato ke nan ya bude reshensa na farko a wajen kasar Amurka a kasar Sin, masana'antar da ake sa ran za ta samar da motoci dubu 500 a kowace shekara. Sai kuma a ranar 11 ga wata, magajin garin birnin Chicago na kasar Amurka ya jagoranci babbar tawagar cinikayya zuwa birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, inda ya daddale "yarjejeniyar hadin gwiwa daga shekarar 2018 zuwa 2023", inda kuma aka yanke shawarar gudanar da hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu a muhimman fannonin da suka hada da kiwon lafiya da kera kayayyakin zamani da kirkire-kirkiren sabbin fasahohi da hada-hadar kudi da ayyukan gona da abinci da manyan ayyuka da sauransu, yarjejeniyar da za a aiwatar cikin shekaru biyar-biyar na farko da aka daddale tsakanin kananan hukumomi na kasashen biyu.

A yayin da fadar White House ke kara kafa shingayen cinikayya ga kasar Sin tare da sa masu sayayyanta biyan karin kudade, yadda kamfanonin kasar ta Amurka suka yi ta zuwa nan kasar Sin don neman damar hadin gwiwa mai dorewa ya shaida cewa, duk da matakan kariyar ciniki da fadar White House ke dauka, kananan hukumomin kasar da kamfanoninta na daukar matakai na nuna adawa da yakin cinikayya, matakin da ya bayyana imaninsu ga kasuwannin kasar Sin. Wasu kungiyoyin 'yan kasuwar Amurka da ma 'yan majalisa ma sun soki sabon matakin sanya harajin da gwamnatin kasar ta dauka, wadanda suka bayyana cewa, "Amurkawa ne za su dandana kudarsu".

A hakika, 'yan siyasa da 'yan kasuwa da ma wadanda ba su san hawa ba balle sauka na kasar ta Amurka suna ta kara gano ainihin halin yakin cinikayya da White House ta tada, wato fadar White House na yanke shawara ne kawai domin gwagwarmayyar jam'iyyu, kuma tana neman cin zabe ne ba tare da yin la'akari da muradun jama'a ba. A yayin da matakan da ta dauka ke kara haifar da illoli, karin Amurkawa na tunani kan cewa, ina suka dosa karkashin gwamnati da hankalinta ya gushe da shure-shuren hauka? (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China