in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin NATO za su kyautata tsarin tafiyar da kungiyar
2018-07-12 10:53:47 cri
Shugabannin kasashen kungiyar tsaro ta (NATO) sun kuduri aniyar kyautata tsarin bayar da kason kudaden tafiyar da harkokin kungiyar, kamar yadda aka wallafa a yarjejeniyar taron kolin kungiyar na baya bayan nan a jiya Laraba.

Yarjejeniyar taron kolin ta ce za'a yi raba daidai na nauyin tafiyar da kungiyar tsakanin mambobin kungiyar, da yin hadin gwiwa wajen tafiyar da kungiyar, da yin gaskiya, da kuma kokarin cimma muradun kungiyar karkashin doka ta 3 da doka ta 5 na kungiyar.

Babban sakataren kungiyar tsaron NATO Jens Stoltenberg, ya fadawa taron manema labarai bayan taron kolin cewa, dukkaninsu sun amince ba'a yin adalci wajen tafiyar da alhakin gudanarwar kungiyar a halin yanzu. Dukkanninsu sun amince cewar ana bukatar makudan kudade a kasafin kudi na tsaro; da karin kwarewa ta zamani; da kuma karin gudunmmawa wajen tafiyar da harkokin kungiyar. Babban abin farin ciki shi ne ana samun ci gaba.

A cewar yarjejeniyar, dukkan mambobin kungiyar sun fara yunkurin kara yawan kudaden da suke kashewa a fannin tsaro a zahiri, kuma kaso biyu bisa uku na kasashe mambobin suna kokarin ware kashi biyu bisa 100 na yawan ma'aunin tattalin arzikinsu na (GDP) a fannin tsaro nan da shekarar 2024. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China