in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a yi taro tsakanin shugabannin JKS da na jam'iyyun kasa da kasa kan batun Afrika a Tanzaniya
2018-07-12 10:50:06 cri
Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin JKS za ta kira wani taro tsakaninta da jam'iyyun kasa da kasa kan batun Afrika daga ran 17 zuwa 18 ga wannan wata a birnin Dares Salaam na kasar Tanzaniya, bisa taken "Matakai da dabaru da jam'iyyun kasashen Afrika suke dauka na neman ci gaba bisa halin da suke ciki", taron da ake sa ran zai samu halartar shugabannin jam'iyyu ko kungiyoyin siyasa na Afrika kimanin 40.

Rahotanni na cewa, an kira wannan taro ne don tabbatar da matsayar da aka cimma game da kara tuntubar JKS da jam'iyyun kasa da kasa da aka yi a watan Disamba na bara. Haka kuma taron zai share fagen taron kolin dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika da zai gudana a watan Satumba a birnin Beijing na kasar Sin. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China