Tsarin daukar fararen hula aikin soja wanda hukumar kolin sojan ta amince da shi, ya kasance irinsa na farko tun da aka fara aiwatar da shirin yin gyare-gyare a harkokin tsaron kasa da na sojojin kasar a karshen shekarar 2015.
Karkashin wannan shiri, a wannan shekara rundunar sojan kasar na fatan daukar fararen hula da suka kware a wasu fannoni domin ba su damar rike wasu muhimman gurabe a rundunar.
Masu sha'awa suna iya aikewa da bukatunsu na neman wadannan gurabe ta shafin intanet daga ranar 12-22 ga wannan wata na Yuli, kana za a shirya jarabawa a ranar 26 ga watan Agusta. Ana fatan kammala daukar ma'aikatan a karshen wannan shekara.
Kafin haka, za a sanar da jama'a game da guraben aikin,ka'idoji da tsari da matakan da za a bi wajen zabar wadanda suka cancanta, domin nuna adalci. (Ibrahim)