in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Koriya ta arewa ta samu ci gaba a fannin martaba bil Adama ko da yake da sauran rina a kaba
2018-07-11 21:24:44 cri

Sakatare mai lura da harkokin kare hakkin bil Adama, da tsare tsaren bada agajin gaggawa na MDD Mark Lowcock, ya bayyanawa wani taron manema labarai cewa, ya zanta da wasu jami'an Koriya ta arewa, kuma kasar ta samu ci gaba mai armashi a fannin kare hakkin bil Adama, tun daga shekarar 2012 kawo yanzu. To sai dai kuma ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba, game da kalubalen da kasar ke fuskanta, wajen samar da abinci mai gina jiki ga yara kanana, da matsalar ruwan sha mai tsafta da magunguna da take fuskanta.

Mr. Mark Lowcock, ya ce gamayyar kasa da kasa sun auna tasirin ci gaban da kasar ta samu a wannan fanni, da kuma irin kalubalen dake gaban ta a halin yanzu. Ya ce Koriya ta arewa za ta samu tallafin dalar Amurka miliyan 110 daga kasashe mambobin MDD.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China