in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Algeria
2018-07-11 21:19:13 cri

Babban dan majalissar zartaswar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Algeria Abdelkader Messahel a Larabar nan.

Yayin ganawar ta su, jami'an biyu sun jaddada kyakkyawan kawancen dake tsakanin kasashen su, da batun zurfafa hadin gwiwa game da shawarar ziri daya da hanya daya, da kuma fadada ci gaba a sassa daban daban. Da yake tsokaci game da hakan, Mr. Wang ya ce yana fatan sassan biyu za su karfafa musaya ta al'ummun su yadda ya kamata.

A nasa bangaren, Messahel ya ce Algeria a shirye take ta aiwatar da dukkanin ayyukan da suka jibanci shawarar ziri daya da hanya daya, za kuma ta bunkasa hadin gwiwa da Sin a sassan da suka hada da raya masana'antu, da cinikayya, da samar da ababen more rayuwa.

Kaza lika sassan biyu sun amince da bukatar kasa da kasa, su ba da goyon bayan wajen raya sha'anin mu'amala tsakanin sassan daban daban, da kare darajar dokokin kasa da kasa, su kuma shiga a dama da su a harkoki na tafiya tare, maimakon bin ra'ayin kashin kai, da nuna danniya a fannin tattalin arziki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China