in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayyana Afrika a matsayin mai kyakkyawar makoma
2018-07-11 11:13:02 cri
Tsohon shugaban hukumar kula da ayyukan Tarayyar Turai Jose Manuel Durao Barroso, ya ayyana nahiyar Afrika a matsayin mai kyakkyawar makoma.

Jose Durao Barroso ya bayyana haka ne yayin da aka bude taro karon farko tsakanin nahiyar Turai da Afrika, a Estoril dake kusa da birnin Lisbon na Portugal.

Kamfanin dillancin labarai na Portugal wato Lusa, ya ruwaito Jose Durao Borroso na cewa, Afrika za ta zama kasuwa mafi girma a duniya dake dauke da mutane daban daban.

Ya ce ya yi imanin cewa, Afrika za ta samu gagarumin ci gaba cikin shekaru kalilan masu zuwa, inda ya ce nahiyar na da kyakkyawar makoma, idan ta samu karin ilimi da kayakin more rayuwa tare da kara girmama dokoki da ka'idoji.

Ya kara da cewa, abokiyar hulda da ta fi dacewa da Afrika ita ce Turai, sai dai ya gargadi Turan da ta kauracewa amfani da dabarun nuna iko akan Afrikar.

An tsara taron na yini guda game da Turai da Afrika ne domin karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu. Taken taron na bana wanda aka yi a karon farko, shi ne "kirkiro da hadin gwiwa domin samar da sauyi". (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China