A cikin makoni masu zuwa, masu yada kimiyar aikin gona daga jihar Morogoro da jami'an ma'aikatar sha'anin noman kasar a wannan fanni su kimanin 40 za su tattauna da shehunnan malamai daga jami'ar koyon ilmin noma na kasar Sin kan fasahohin dake da nasaba da aikin noma, alal misali, shuke-shuke na zamani, da kiwon tsuntsaye da rigakafi da shawo kan wasu cututuka, na'urorin aikin gona, sarrafa abinci, da ingancin abinci da dai sauransu.
Rahotanni na cewa, a shekarun nan baya-baya, hadin kai tsakanin Sin da Afrika ta fuskar aikin noma karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya" da Sin take gabatar da dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrik ya bunkasa kwarai, kuma aikin ya samu ci gaba mai armashi. Ya zuwa karshen shekarar 2017, masu kula da kwararru da masana kimiyyar kasar Sin sun gudanar da ayyukan gwaje kimanin 300 a kasashen Afrika 9, tare da yada fasahohin aikin gona har 450, da horar da manoma da masanan wurin da yawansu ya kai kusan dubu 30. (Amina Xu)