in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Cote d'Ivoire ya nada sabbin ministocinsa
2018-07-11 10:40:23 cri

A jiya ne shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya ba da umurnin nada ministoci 35 da sakatarori 5, matakin dake nuna cewa, an kafa sabuwar gwamnati.

Babban sakatare a fadar shugaban kasar Patrik shi ne ya sanar da jerin sunayen ministocin a yayin wani taron manema da aka shirya a jiyan.

Bayan gwambawul da gwamnatin ta yi, yanzu haka akwai shugabannin hukumomi 10, ciki hadda ma'aikatar kiwon lafiya, ma'aikatar ba da ilmi da nazarin kimiya da dai sauransu.

Sabuwar gwamnati dai na kunshe da mambobi 41, ciki har da sakatarori 5 maimakon mambobi 35 a gwamnatin da ta gabata, haka kuma an nada mata 7 a cikin sabuwar gwamnatin.

A ranar 4 ga wata ne, Alassane Ouattara ya ba da umurnin shugaba guda 2, daya daga cikinsu shi ne rushe gwamnatin dake karkashin jagorancin Amadou Gon Coulibaly, na biyu kuma shi ne sake nada Coulibaly a matsayin sabon firaministan kasar, da ba shi nauyin kafa sabuwar gwamnatin. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China