in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya caccaki kasashen Turai gabanin gudanar da taron kungiyar tsaro ta NATO
2018-07-11 10:34:43 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump yana cigaba da yin kakkausar suka kan shugabannin kasashen Turai a yayin da ake gaf da fara taron kolin kungiyar tsaro ta (NATO) a birnin Brussels na kasar Belgium.

Trump wanda tuni ya isa birnin Brussels da yammacin jiya Talata domin halartar taron kolin na NATO, wanda aka tsara gudanar da shi a ranakun Laraba da Alhamis, kana daga bisani zai kai ziyara kasar Birtaniya inda kuma daga can zai gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a Helsinki babban birnin kasar Finland.

Da yammacin jiya Talata shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na tweeter yana cewa "Kungiyar tarayyar Turai sun hana manomanmu, da ma'aikatanmu, da kamfanoninmu yin cinikayya da Turai, Amurka tana fuskantar gibin ciniki na kimanin dala biliyan 151, kuma yanzu su ce suna son mu ne zamu ba su kariya ta hanyar kungiyar NATO, kuma mu biya musu kudade haka siddan. Sam wannan ba za ta samu ba!"

A wani karin sakon tweetar na mista Trump ya ce "Kasashe da dama na NATO, wadanda ake sa ran za su ba da tsaro, ba wai suna rage azamarsu da kashi biyu bisa 100 ba ne wanda shi ne mafi karanci, har ma suna kaucewa biyan kudaden da ya kamata su bayar shekaru masu yawa da suka gabata. Shin ko za su sake maidawa Amurka kudin ne?" In ji shugaban kasar Amurka. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China