Wang wanda ya bayyana hakan yayin da yake shugabantar taron dandalin ministocin Sin da kasashen Larabawa, ya ce Sin da kasashen Larabawa sun kara fadada alakar dake tsakaninsu karkashin shawarar Ziri daya da Hanya daya. Kana kasar Sin tana kokarin bude kofa ga kasashen waje yayin su kuma kasashen Larabawa ke kara zamanatar da masana'antu da fadada tattalin arzikinsu.
Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, muhimman fannoni guda uku da aka amince da su a yayin ganawar, sun hada da sanarwar Beijing, da matakan da za a dauka game da hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa a fannin shawarar ziri daya da hanya daya, da matakan da aka tsara daga shekarar 2018 zuwa 2020 don kara bunkasa wannan dandali, kundin da ya yi bayani dalla-dalla game da yadda za a bunkasa alakar Sin da kasashen Laraba a nan gaba.(Ibrahim)