Ya ce nasarorin da aka samu karkashin hadin gwiwar zai taimaka wajen daga matsayin kyakkyawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika.
Taron dandalin hadin gwiwar tsaron na Sin da Afrika wanda shine irinsa na farko, ya samu halartar wakilan gwamnatin Sin, da kasashen Afrika da kuma kungiyar tarayyar Afrika, wanda aka bude shi tun a ranar 26 ga watan Yuni kana aka kammala taron a jiya Talata.
Wakilan kasashen Afrika da suka halarci taron sun bayyana kyakkyawar fatansu na yin hadin gwiwa tsakanin kasashensu da kasar Sin a aikace daga dukkan fannoni.
A taron dandalin, wakilan sun tattauna tare da cimma matsaya game da batutuwan da suka shafi yadda za'a kyautata makomar rayuwar al'ummomin Sin da kasashen Afrika a nan gaba da kuma karfafa hadin gwiwa Sin da Afrika a fannin aikin soji a sabon zamani. (Ahmad)