in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Hadin kan Sin da Turai ya sanya sabon karfi ga tattalin arzikin duniya
2018-07-10 20:19:58 cri

Firaminitan kasar Sin Li Keqiang ya ziyarci kasashen Bulgaria da Jamus tsakanin 5 zuwa 10 ga watan nan na Yuli, inda ya halarci taro karo na 7 na ganawar shugabannin kasashen Sin da kasashen da ke tsakiya da gabashin Turai, gami da shugabantar shawarwari karo na biyar, a tsakanin gwamnatocin Sin da Jamus a birnin Berlin.

Hadin gwiwa a tsakanin Sin da Turai zai taimaka wajen karfafa hadin kan karfi biyu, da manyan kasuwannin biyu, da al'adun sassan biyu. Haka nan bangarorin biyu za su taimakawa juna ta fuskar tattalin arziki, da yada fifikonsu, da ma kyautata zamantakewar jama'arsu.

A halin yanzu, rikici na barkewa sakamakon ra'ayin ba da kariyar cinikayya, na kashin kai da Amurka ke dauka. Cin zali a fannin cinikayya da Amurka ke yi na kawo barazana sosai ga tsarin ciniki maras shinge ta duniya, da ma ka'idojin kasa da kasa. Idan ba a dakatar da hakan ba, ko shakka ba bu hakan zai yi illa ga ci gaban tattalin arzikin duniya da ma farfadowarsa.

A wannan muhimmin lokacin da ake ciki, ya kamata Sin da Turai su yi kokari tare, wajen goyon bayan gudanar cinikayya cikin 'yanci, da saukaka aikin zuba jari, domin kiyaye tsarin tattalin arziki mai bude kofa ga waje, da na ciniki a tsakanin bangarori daban daban.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China