in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya dace a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa
2018-07-10 19:42:27 cri

A yau Talata 10 ga watan nan ne aka kaddamar da taron ministoci karo na 8, na dandalin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa a nan birnin Beijing. A cikin shekarun baya bayan nan, huldar dake tsakanin sassan biyu na gudana lami lafiya, ba ma kawai a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ba, har ma da fannin fahimtar juna.

Game da huldar dake tsakanin kasar Amurka da kasashen Larabawa kuwa, a bayyana take, an ga kasashen Larabawa suna nuna adawa da Amurka, musamman ma kasashen dake yankin Gabas ta Tsakiya. To, ko mene ne dalilin da ya sa huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa kara kyautatuwa sannu a hankali?

Hakika dalilin yana da nasaba da fannoni da dama, amma abu mafi muhimmanci shi ne, har kullum kasar Sin na nacewa manufar rashin tsoma baki a cikin harkokin gida na sauran kasashe, haka kuma ta nacewa manufar warware rikici ta hanyar siyasa, da manufofin da suka samu amincewa daga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

A halin da ake ciki yanzu, yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki yana da sarkakiya, idan kasashen suna son shimfida zaman lafiya a fadin yankin, dole ne su nuna kiyayya ga akidar nuna fin karfi na kasashen yamma. A don haka kasar Sin tana mayar da kanta a matsayin kasa mai himmantu kan aikin shimfida zaman lafiya a yankin, amma ba mai tayar da rigingimu ba.

Domin aiwatar da manufar harkokin diplomasiyya mai halayyar musamman ta kasar Sin a yankin Gabas ta Tsakiya, misali a tsara tsarin manzon musamman da shiga aikin kiyaye zaman lafiya a yankin. Kana a cikin aikin mafi jawo hankalin jama'a shi ne shirya dandalin hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa a shekarar 2004. Kawo yanzu sassan biyu sun riga sun shirya taron ministoci har sau shida, haka kuma sun samu babban sakamako.

Yanzu haka kasashe masu tasowa suna fuskantar rikici, da kalubale da dama, shi ya sa akwai bukata kasar Sin da kasashen Larabawa su kara karfafa cudanya, da hadin gwiwa dake tsakaninsu, domin samun makoma mai haske a nan gaba. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China