in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi jawabi a wajen bikin bude taron ministoci na dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa
2018-07-10 15:23:48 cri

A yau 10 ga wata, aka bude taron ministoci karo na 8 na dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron tare da gabatar da wani jawabi mai taken "hadin gwiwa don ciyar da huldar dake tsakanin Sin da kasashen Larabawa gaba", inda ya sanar da cewa, kasar Sin da kasashen Larabawa sun riga sun cimma matsaya, wajen kafa wata huldar abota da ta shafi manyan tsare-tsare tsakanin bangarorin 2, wadda za ta tabbatar da hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, da yunkurinsu na neman samun ci gaba tare, don samun makoma mai haske.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, shawarar "Ziri daya da Hanya daya" da kasar Sin ta gabatar tana samun karbuwa sosai a tsakanin gamayyar kasa da kasa, musamman a kasashen Larabawa. Kasashen sun kasance a inda "Ziri daya" ya hadu da "Hanya daya", don haka su ne kasashen da ake yawan hadin gwiwa da su yayin da ake aiwatar da shawarar "Ziri daya da Hanya daya".

Haka zalika, shugaban kasar Sin ya ce, kasar Sin da kasashen Larabawa dukkansu na taka muhimmiyar rawa wajen kula da harkokin siyasa na kasa da kasa. Ganin haka ya sa shugaban ya yi kira ga kasashen Larabawa da su yi nazarin yanayin tarihi, da mayar da martani ga bukatun jama'a, ta yadda za a samu damar farfado da tattalin arzikin yankin gabas ta tsakiya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China